rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lagos Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Legas zata rushe babbar mayankar jihar

media
Wani sashi na babbar mayankar dabbobi ta jihar Legas da ke karamar hukumar Agege, Najeriya. BusinessDay

Gwamnatin Lagos a Najeriya ta umurci masu sayar da dabbobi a babbar mayakan jihar wato abbatoir da ke Agege, da su tattara nasu ya nasu su bar wurin, domin za a rusa wurin nan ba da jimawa ba.


Hakan yasa shugabancin ‘yan kasuwar dabbobin suka bukaci masu fataucin shanu daga arewa zuwa Lagos da su dakatar da wannan fatauci har sai abin da halin ya yi.

Har yanzu dai gwamnatin jihar ta Lagos bata kayyade wa’adin da ta debawa masu gudanar da sana’arsu a mayankar ba.

Wannan matakin ne yasa yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Alhaji Abdullahi Liliga, shugaban Miyatti a jihar ta Lagos, ya bayyana cewa matakin tamkar bita da kulli gwamnati ke nufinsu da shi, kasancewar hatta wurin wucin gadin da ta basu a yanzu kuma ta ce shima rusa shi zata yi.

Gwamnatin Legas zata rushe babbar mayankar jihar 07/05/2018 - Daga Abdoulkarim Ibrahim Saurare

Bincike ya nuna cewa akalla shanu da sauran dabbobi, 8,000 ne ake yankawa kowace rana Lagos, wadanda aka kiyasta kudinsu zai kai Naira biliyan daya da rabi.