Isa ga babban shafi

An fara taron raya yankin tafkin Chadi

An fara taron gwamnonin jihohi da ke amfana da tafkin Chadi, da kuma masu ruwa da tsaki wajen kokarin farfado da tattalin arzikin yankin na shekarar 2018.

Zauren taron gwamnoni da masu ruwa da tsaki akan farfado da tattalin arziki da tsaron yankin tafkin Chadi.
Zauren taron gwamnoni da masu ruwa da tsaki akan farfado da tattalin arziki da tsaron yankin tafkin Chadi. RFI
Talla

Taron na kwanaki biyu zai gudana ne a garin Maduguri da ke jihar Borno daga ranar 8 zuwa 9 ga watan Mayu.

Gwamnoni 11 ne da jihohinsu ke cutuwa da kafewar tafkin Chadi ke jagorantar taron, domin tattaunawa muhimman batutuwan da suka shafi inganta tsaro a tsakanin iyakokinsu, da kuma maido da karsashin kyakkyawan tattalin arzikin sa yankin tafkin Chadi ke amfana da shi a baya.

Jihohin dai sun hada da gwamnonin jihohi 6 na yankin arewa maso gabashin Najeriya, sai kuma gwamnoni guda daga kasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar, da kuma guda daya daga Kamaru da ke halartar taron.

Daga cikin sauran manyan jagororin da ke halartar taron raya tafkin na Chadi akwai, wakilin majalisar dinkin duniya na musamman, Dr. Muhammad Ibn Chambas, da kuma sakatare janar na Majalisar dinkin duniya mai lura da yammacin Afrika, Francois Lounceny Fall.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.