Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun kubutar da mutane fiye da 1,000 daga hannun Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto karin sama da mutane 1,000 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Sojin Najeriya, yayinda suke taimakawa wasu mutane da suka ceto daga sansanonin mayakan Boko Haram.
Sojin Najeriya, yayinda suke taimakawa wasu mutane da suka ceto daga sansanonin mayakan Boko Haram. Reuters
Talla

Daraktan sashin hulda da jama’a na rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ne ya bayyana haka cikin sanawar da ya rabawa manema labarai.

Birgediya Chukwu ya ce an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su ne daga kauyukan Malamkari, Amchaka, Walasa da kuma Gora dukkaninsu a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Mafi akasarin wadanda sojin suka ceto daga hannun mayakan na Boko Haram mata be da kananan yara, sai kuma wasu matasa da aka tilastawa zama mayakan kungiyar ta Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.