rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Birtaniya Muhammadu Buhari Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babu tabbacin ranar dawowar Buhari daga London

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mukarrabansa REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo

Fadar shugaban Najeriya ta ce, ba za ta iya bada tabbaci ba kan cewar, shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida daga birnin London a ranar Asabar mai zuwa kamar yadda aka tsara tun farko.


Mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana haka a yayin zantawa ta wayar tarho da kafar talabijin ta Channels da ke kasar.

A farkon wannan makon ne shugaba Buhari ya koma birnin London don duba lafiyarsa, yayin da ake saran dawoarsa a ranar Asabar kafin kuma ya kai ziyara jihar Jigawa da ka arewacin Najeriya a ranar Litinin.

Kawo yanzu fadar shugaban ba ta bada bayani ba kan irin rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita, lamarin da fadar ke cewa, wani al’amari ne da ya shafi rayuwar mutun.

A shekarar da ta gabata ne, shugaba Buhari mai shekaru 75 da haihuwa ya shafe tswon watanni hudu yana jinya birnin London.