rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ebola Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ebola: Jami'an Najeriya sun fara sa ido akan lafiyar fasinjoji

media
Wasu jami'an lafiya na kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins sans Frontieres (MSF), yayin aiki a wata cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola, Kailahun da ke kasar Saliyo. REUTERS/Tommy Trenchard

Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta dauki matakan shirin ko ta kwana, inda ake na sa ido akan shigi da ficen jama’a a akan iyakokin kasar da kuma filayen jiragen sama, bayan samun rahoton sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.


Zuwa yanzu kuma cutar ta Ebola ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 17 a kasar.

Ministan lafiya na Najeriya, Isaac Adewole ya ce za a rika bin matakai masu tsauri don tantance fasinjojin da ke shiga kasar, musamman wadanda suka fito daga Jamhuriyar Congo.

Wannan dai shi ne karo 9 da aka sake samun bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Congo, tun bayan fara bayyanarta a shekarar 1976.

A shekarar 2014 ne cutar Ebola ta hallaka kusan mutane 11,000 bayan bullar da ta yi a kasashen Liberia, Saliyo da kuma Guinea.