rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta biya masu fallasa kudaden sata 14 hakkinsu

media
Ministar Kudin Najeriya Kemi Adeosun. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta biya wasu ‘yan kasar 14, ladan naira miliyan 439, sakamakon yadda suka taimakawa gwamnatin, wajen karbo kusan naira biliyan 14 daga masu gujewa biyan kudaden haraji.


Yayin da take karin bayani akan biyan kudaden, ministar kudin Najeriya Mis Kemi Adeosun ta ce kyautar ta banbanta da wadda aka fi ta karrama masu fallasa kudaden sata, kasancewar mutanen 14 sun taimakawa gwamnati ne wajen fallasa masu kaucewa biyan gwamnati haraji.

Ministar ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana kan shirin gurfanar da masu aikata lafin kin biyan haraji a kotu, nan da zuwa karshen watan da muke ciki, a lokacin da wa’adin yiwa masu aikata lafin afuwa zai kare.

Adeosun ta ce tun bayan da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da fara amfani da shirin fallasa masu kin biyan haraji da aka yi wa lakabi da VAIDS a shekarar 2017, an bankado jimillar kamfanoni da kuma attajirai sama da 130,000 da suka aikata laifuka kaucewar biyan haraji.

A bangaren masu fallasa kudaden haramun ko na sata kuma, Ministar kudin ta ce zuwa watan Yuni na shekarar 2017 da ta gabata, gwamnatin Najeriya ta samu biyan naira miliyan 375, 875 ga wadanda suka wasu mutane 20 da suka taimaka wajen kwato kudaden sata da yawansu ya kai naira Biliyan 11, da miliyan 635,000,000.