Isa ga babban shafi
Kano

An yi jana'izar marigayi Shiekh Isyaka Rabi'u

A ranar Juma’a aka yi jana’izar marigayi Shiek Isyaka Rabi’u, shugaban darikar Tijjaniya na Afrika, a masallacinsa da ke goron dutse a jihar Kano, Najeriya.

Gawar Marigayi Sheik Isyaku Rabiu, shugaban Darikar Tijjaniya na Afrika, a lokacin da ake kokarin yi masa jana'iza.
Gawar Marigayi Sheik Isyaku Rabiu, shugaban Darikar Tijjaniya na Afrika, a lokacin da ake kokarin yi masa jana'iza. Solacebase
Talla

A ranar Talata da ta gabata, Shiekh Isyaka Rabi’u ya rasu a birnin London bayan fama da jiyya, yana da shekaru 93.

Limamin Masallacin Kaulaha Shiekh Tijjani Aliyu Sisa ne ya jagoranci yi wa marigayin Sallah, daga bisani aka kaishi makwancinsa.

Daga cikin manyan mutanen da suka samu halartar jana’izar marigayi Shiekh Isyaka Rabi’u, akwai Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar ganduje, da mataimakinsa Farfesa Hafiz Abubakar, da kuma gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar.

Sauran manyan da suka halarci jana’izar sun hada da Ministan cikin gida na Najeriya, Janar AbduRahman bello Dambazau, babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk, da kuma Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahmud Ringim.

Domin karramashi ne gwamnatin Kano, ta sauya sunan asibitin kananan yara da ke yankin Zoo Road a jihar zuwa sunan marigayin malamin wato Asibitin Khalifah Shiekh Isyaka Rabi’u.

Al’ummah zata rika tuna marigayi Shiekh Isyaka Rabi’u da shahararsa a fagen ilimi, Karatun Al-Qur’ani mai girma da hidimta masa, taimakon al’umma da kuma shahara a fagen kasuwanci.

Shiekh Isyaka Rabi’u ya rasu ya bar mata guda hudu da ‘ya’ya 63.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.