rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ku nemi watan Ramadan a ranar Laraba- Sarkin Musulmi

media
Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar Daily Trust/Nigeria

Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Addin Islama a Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci Musulman da ke sassan kasar da su nemi jinjirin watan Ramadan a ranar Laraba mai zuwa.


Wata sanarwa da mataimakin Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar ta ce, biyo bayan shawarar da kwamitin neman wata ya bayar, Sarkin Musulmin ya bukaci mabiya addinin Islama a kasar da su gaggauta fara neman watan jim kadan da faduwar rana a ranar 16 ga watan Mayu na shekarar 2018, wato wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Sha’aban na shekarar1439 da hijiran manzan Allah S.A.W.

Sanarwar ta ce, da zaran nagartattun Musulmai sun hangi watan a yammacin ranar ta Laraba, to Sarki Sa’ad zai ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.

Sai dai idan aka gaza hangen watan a ranar ta Laraba, to babu shakka Juma’a za ta kasance kai tsaye ranar farko a cikin watan na Ramadan kamar yadda sanarwar Sarkin ta bayyana.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu daga cikin mambobin Majalisar Kolin da za a tuntuba da zaran an hangi watan da suka hada da Mallam Hafiz Wali (08036009090) da Sheik Dahiru Bauchi (08032103733) da Sheik Kariballah Kabara (08035537382) sai Muhammad Nasir AbdulMuhyi (08065687545).

Sauran Malam da za a tuntunba sun hada da Sheik Bala Lau (08037008805) da Sheik Sani Yahya Jingir (08065687545).