rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zamfara ta kona bindigogi kusan dubu 6 na 'yan ta'adda

media
Reuters

Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta yi bikin kona bindigogi kusan 6,000 da ta karbe daga hannu 'yan bindiga a karkashin shirinta na afuwa.


Bikin ya samu halartar jami’an Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma da kuma wakilan gwamnatin tarayya.

A zantawarsa da sashen hausa na RFI Ibrahim Dosara, mai bai wa gwamnan jihar Abdulaziz Yari shawara kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa, an dauki matakin kona makaman ne don hana sake yaduwarsu tsakanin ‘yan ta'addan da ke hallaka jama’a.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren cikakkiyar hira da Ibrahim Dosara kan kona makaman a Zamfara.

Ibrahim Dosara kan kona makamai a Zamfara 15/05/2018 Saurare

Dosara ya kara da cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da tattaunawa a karkashin shirin na afuwa da zimmar kwance damarar sauran 'yan ta'addan da ke dauke da makamai don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Jihar Zamfara dai na fama da munanan hare-haren ‘yan bindiga da ke kai ga asarar dimbin jama’a lokaci zuwa lokaci.