rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gambia Hakkin Dan Adam Yahya Jammeh Ghana Najeriya Senegal Togo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zargin Yahya Jammeh da kisan 'yan Afrika 50 a Gambia

media
Rahotanni sun ce mutanen sun fito ne daga kasashen Najeriya Ghana Togo da kuma Senegal. REUTERS/Thierry Gouegnon

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun zargi tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh da bai wa wata runduna da ke karkashin sa umarnin kashe wasu baki yan kasashen Afirka ta Yamma 50 a shekarar 2005.


Kungiyar Human Rights Watch da TRIAL International sun ce sun yiwa wasu tsoffin jamiā€™an gwamnatin Gambia 30 tambayoyi akai, cikin su harda sojoji 11 da kuma wani da ya tsallake rijiya da baya daga harin, kuma sun tabbatar mata da kisan.

44 daga cikin bakin sun fito ne daga Ghana da Najeriya da Senegal da kuma Togo, wadanda ke neman zuwa Turai ta teku.

Kungiyoyin sun ce an kama su ne a gabar ruwan Banjul inda aka mika su ga rundunar da ke karkashin shugaban wadda ta hallaka su.

Wani bincike da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya suka gudanar a shekarar 2009 ya tababtar da cewar rundunar da ake zargin ce ta kashe su.