rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon tsarin taimakawa juna tsakanin Maradi da Katsina

media
Kofar shiga garin Maradi a Nijar via-linternaute.com

Jihohin katsina a Najeriya da Maradi a Nijar sun bude wani taro na gabatarwa abokan hulda tsarin da sukayi na aiki don kawo karshen rigingimu tsakanin manoma da makiyaya a yankunan biyu, a wani hadin gwiwar da suka kulla na aiki tare tsawon shekaru uku masu zuwa.


Matsalolin rashi tsaro a Zamfara na daga cikin batutuwan da wannan taro ya maida hankali a kai, sakamakon cikas din da wasu makiyayan Nijar suka fara samu.

Hukumomin jihohin biyu sun dau alkawakin dafawa juna a wannan tafiya don kawo karshen matsalolin da yankunan su ke fama da su cikin dan karamin lokaci.