Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin aikata laifuka a Taraba

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da rahoton kwamitin da ta kafa na bincikar zargin da tsohon hafsan sojin kasar Lafatanar janar Theophilus Danjuma ya yi, na cewa, jami’an sojin kasar sun hada kai da makiyaya wajen hallaka mutane da dama na wasu kabilu yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a Jihar Taraba.

Babban hasfan sojin Najeriya Yusuf Tukur Buratai.
Babban hasfan sojin Najeriya Yusuf Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

A ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata, babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya kafa kwamitin mai manbobi 10 don bincika zarge-zargen aikata ba dai dai ba da ake musu.

Rahoton wanda Manjo Janar Nuhu Angbaso ya bayyana a madadin Hafsan sojin kasar, ya ce babu inda aka samu rahoton sojin sun goyi bayan wani bangare, zalika a lokuta kalilan ne aka tsinkayi sojin Najeriyar sun shiga tsakani don sansanta rikici tsakanin fararen hula da bai shafi barazanar tsaron kasa ba.

Zalika rahoton ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin sojin Najeriya da dukkanin hukumomin tsaron da aiki a jihar ta Taraba.

Kari daga cikin batutuwan da rahoton rundunar sojin Najeriyar ya bayyana akwai gano matsalar rashin tsaro akan iyakar Kamaru da jihar ta Taraba, daya daga cikin dalilan da suka bada gudunmawa wajen yaduwar kananan makamai a tsakanin kabilun jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.