Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun dakile yunkurin kai harin kunar bakin wake a Kawuri

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar dakile yunkurin wasu ‘yan kunar bakin wake mata, da suka yi kokarin kaiwa sojoji hari a Kawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation Lafiya Dole Kanal Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar jiya Asabar, wadda ta ce an yi yujkurin kai harin ne a daren Juma’ar da ta gabata.

Nwachukwu ya ce ‘yan kunar bakin waken na gaf da kutsawa cikin sansanin sojin na Kawuri, sojoji da jami’an Vigilante sukai kokarin tsare su, a nan ne bam da ke jikin daya daga cikin matan ya tarwatse tare da hallaka ‘yan kunar bakin waken 2.

Daga bisani kwararru sun kwance bam din da akai sa a da bai riga ya tashi ba, da ke jikin damarar daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.