rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Najeriya Bauchi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mataimakin gwamnan Bauchi ya yi murabus

media
Eng. Nuhu Gidado da ya yi murabus daga kujerar mataimakin gwamnan Bauchi twitter.com/nuhugidado

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi da ke Najeriya, Eng. Nuhu Gidado ya yi marabus daga mukaminsa.


A wasikar murabus din da ya rubuta wa gwamnan jihar Mohammed Abubakar, mataimakin gwamnan mai marabus ya ce, da ma tun da farko ya yi alkawarin zai rike wannan matsayi ne don yin wa’adi sau daya, to sai dai sakamakon wasu matsaloli da ke faruwa a yanayin mulkin jihar ta Bauchi, ba zai iya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wannan wa’adi ba.

A watan Disambar da ya gabata ne kwamishin kudi da tsare-tsare na jihar, Shehu Ningi ya yi marabus daga nasa mukamin, yayin da mai bai wa gwamna shawara kan zuba jari, Samaila Sanusi ya dauki irin wannan mataki a watan Maris, dukkaninsu suna zargin cewa gwamnan ba ya sauraren abokan aikinsa.

Sai dai a yayin da rahotanni ke cewa, Eng. Gidado ya yi murabus ne saboda rashin gamsuwa da salon jagorancin gwamnan, makusantan gwamnan sun ce,mataimakin ya yi murabus ne ba tare da wani gamsasshen dalili ba, illa kawai yana da matukar buri a ransa.

Ba kasafai ake samun mataimakin gwamna da ke murabus daga kujerarsa a Najeriya ba.