rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zamfara Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun kai hari kan garin Zanuka da ke jihar Zamfara

media
Yankin Bawar Daji a Zamfara na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan bindiga. Information Nigeria

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin barayin shanu ne, sun kai hari a garin Zanuka, da yankin Bawar Daji, da ke jihar Zamfara, a inda suka hallaka mutane sama da 23.


Shugaban karamar hukumar Anka dake jihar ta Zamfara, Alhaji Gado Mustafa ya ce ‘yan bindigar sun kuma kone gidaje da dama a harin da suka kai.

Yayin zantawar shi da Bashir Ibrahim Idris ta wayar tarho Alhaji Gado Mustafa ya ce a halin da ake ciki mutanen yankin suna cikin halin fargaba, la’akari da cewa ‘yan bindigar suna gargadin manoma da cewa su kauracewa ayyuka a gonakinsu, muddin suka ki bin umarni kuma su hallaka su, ko su yi garkuwa da su, har sai an biya kudaden fansa.

Shugaban karamar hukumar Anka Alhaji Gado Mustafa 02/06/2018 - Daga Bashir Ibrahim Idris Saurare