rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saraki na iya rubuto amsar zarge-zaren da ake masa inji ‘yan Sanda

media
Nigeria Senate President Bukola Saraki

A wani mataki na fasa tilasta shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki gurfana a gaban rundunar ‘yan sandan kasar akan zargin alaka da ‘yan fashi, hukumar yansandan Najeriya ta bukaci Saraki ya rubuto mata amsa.


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce a halin yanzu ba a bukatar shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki ya gurfana gabanta domin amsa tambayoyi dangane da zargin alaka da wasu ‘yan fashi da suka kashe mutane 33 a jihar Kwara, a maimakon hakan za a aike wa shugaban majalisar dattawan da tambayoyi ne domin karbawa a rubuce cikin sa’o’i 48.

Da fari dai sai da rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta bayyana bukatar Bukola Saraki ya gurfana a gabanta domin lallai ne ya amsa mata wasu tambayoyi musamman da suka shafi wasu shaidun da suka bayyana a fili na wasu abubuwan da 'yan fashin ke amfani da su, sa suka hada da Motoci masu lambobin Saraki baro-baro a gabansu da bayansu.

Sabon matakin na rundunar ‘yan sanda ya biyo bayan ganawar sirri da aka yi ne tsakanin matakaimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, da sufeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris, da shugaban hukumar DSS Lawal Daura a jiya litinin.

To sai dai mutane irinsu Abdulkarim Dayyabu jagoran rundunar adalci a Najeriya, na ganin cewa bai kamata a yi rufa-rufa da wannan batu ba, wannan idan ana so a yi adalci kenan.

Ya ce laifi duka laifi ne, idan aka ce hukunci ya tsaya a kan mutum, zancen a dubi kimarsa ko darajarsa ko matsayinsa, sam bata taso ba.