rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya sauya ranar bikin Dimokaradiya zuwa 12 ga watan Yuni

media
Marigayi Cif MKO Abiola, wanda ya lashe zaben shugabancin Najeriya da ya gudana a watan Yunin shekarar 1993. FRANCOIS ROJON/AFP/Getty Images

Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari, ya sauya ranar bakukuwan kafuwar mulkin dimokaradiyya daga 29 ga watan Mayu, zuwa ranar 12 ga watan Yuni da muke ciki a kowace shekara.


Cikin sanarwar da ya rattabawa hannu da kansa, shugaba Buhari ya ce, za a karrama wanda ya lashe zaben shugabancin Najeriya na ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993, wato Cif Moshood Abiola da lambar girmamawa mafi daraja a kasar GCFR.

Baya ga Abiola, Buhari, ya ce zai karrama mataimakinsa da suka yi takara tare a waccan lokacin, Alhaji Babagana Kingibe, da kuma marigayi Cif Gani Fawehimi, shahararren mai rajin kare hakkin dan adam, da lambar girmamawa ta 2 mafi daraja a Najeriya, wato CFR.

Sanarwar ta ce za a yi bikin karrama jagororin ne a ranar 12 ga watan Yuni da muke ciki.

A cewar shugaba Buhari, ranar 12 ga watan Yuni ta shekarar 1993, ta na muhimmanci ga ‘yan Najeriya fiye da ranakun 29 ga watan Mayu ko 1 ga watan Oktoba, la’akari da cewa a ranar ce aka yi zaben shugabancin kasa mafi tsafta da gaskiya a tarihin Najeriya.