rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta musanta janye gayyatar Saraki

media
Hoton shugaban majalisar dattijan Najeriya da babban Sifeton 'yan sandan kasar Ibrahim Idris. Daily Post

Rundunar ‘yan san dan Najeriya ta ce bata janye gayyatar da ta yi wa shugaban majalisar dattijan kasar Bukola Saraki ba, domin yi mata bayani dangane da alakarsa da wasu gungun ‘yan fashi da suka shiga hannun rundunar.


Yayin da yake sanar da haka a Abuja, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta Najeriya, Jimoh Moshood, ya ce tilas Saraki ya zo da kansa domin wanke kansa dangane da alakarsa da ‘yan fashin.

Gungun masu laifin sun fada komar ‘yan sandan Najeriya ne bayan da suka yi fashi a wasu bankuna da ke garin Offa da ke jihar Kwara, a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata na shekarar da muke ciki, inda suka hallaka mutane da dama, ciki har da jami’an ‘yan sanda 9.

Yayin da yake bayyana karin wasu mutane 2 da suka kama, bisa hannu a fashin na garin Offa, a ranar lahadi da ta gabata, mai magana da yawun ‘yan sandan Jimoh Moshood ya ce, shugabannin gungun masu laifin su bayyana cewa suna da alaka da shugaban majalisar dattijan Najeriyar Bukola Saraki da kuma gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed.

A ranar Litinin da ta gabata, Saraki, ta shafinsa na twitter, ya bayyana cewa, bai samu sakon gayyatar da rundunar ‘yan sandan ke cewa ta yi masa ba, amma daga bisani a dai ranar ta Litinin, shugaban majalisar dattijan ya ce, ya samu sakon ‘yan sandan da ke bukatar ya kare kansa a rubuce.