rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya sa hannu kan dokar bai wa majalisar dokokin jihohi 'yanci

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Stringer

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar da ke bai bangaren shara’a da kuma Majalisar dokokin jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnoni ba.


Mai bai wa shugaban kasar shawara kan batutuwan da suka shafi majalisa Ita Enang, ya ce bayan sanya hannu kan wannan doka, daga yanzu babu wani shamaki ga bangarorin biyu na damar isa ga asusun ajiyarsu ba tare da neman izinin gwamna ba.

Kafin amincewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wannan doka, majalisu da kuma bangaren shari’a na jihohi na fuskantar tsaiko kafin samun kudadensu, sakamakon jinkirin da ake samu daga gwamnoni.