rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Najeriya sun hallaka 'yan bindiga a kauyukan Kaduna

media
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga 12, a wani samame da suka kai kan wasu kasuwannin kauyukan jihar Kaduna.


Cikin sanarwar da ya fitar a jiya Asabar, kakakin rundunar sojin ta 1 da ke Kadunan, Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ce an kai samamen ne kan kauyukan Mai-daro, Kidandan, da kuma Sabon fili, inda ‘yan bindigar masu garkuwa da mutane, suke zuwa domin cin kasuwanni.

Birgediya Janar Chukwu ya ce, sun kuma samu nasarar kwace akalla Babura 32 daga hannun ‘yan bindigar.

Hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna ya yi kamari a shekarar 2018 da muke ciki, inda suka fi shafar karamar hukumar Birnin Gwari, inda mahara suka kone daruruwan gidaje, tare da sace mutane da kuma yin garkuwa da su.