Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnoni basu da iko akan jami'an tsaron da ke Jihohinsu - Abdul'aziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara, kuma shugaban kungiyar gwamnoni ta Najeriya, Abdul-Aziz Yari Abubakar, ya bukaci majalisun tarayyar kasar da su cire wa gwamnoni mukamin da aka lakaba musu na shugabannin jami’an tsaron jihohinsu.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari.
Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari. RFIHAUSA
Talla

Yari ya ce gwamnonin basu da bukatar wannan mukami la’akari da cewa basu da cikakken ikon sarrafa jami’an tsaron da ke jihohinsu, ta hanyar hukuntawa, kora ko kuma daukar sabbin jami’an tsaron, duk da cewa suna amsa mukamin shugabannin jami’an tsaron jihohin na su.

Gwamnan jihar ta Zamfara ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da ya ke nuna bacin ransa dangane da yadda har yanzu ake ci gaba da samun hasarar rayuka masu yawa a jihar, a dalilin hare-haren ‘yan bindiga, duk da aikewa da karin jami’an tsaro.

Bukatar gwamnan na Zamfara na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan jihar ta ce wasu gungun mahara sun hallaka mutane 10, a hare-haren da suka kai kan kauyukan Dutsen-Wake da Oho a karamar hukumar Birnin-Magaji.

Yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani a Gusau a ranar Laraba, kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Muhammad Shehu, ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-haren kan kauyukan da misalin karfe 10 na dare a ranar Talata.

Sai dai DSP Shehu, ya ce a lokacin da jami’an su suka kai wa al’ummar kauyukan dauki, maharan sun tsere zuwa cikin dajin Rugu, wanda ya yi iyaka da jihar ta Zamfara da Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.