rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Najeriya Kwallon Kafa Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Okocha ya dora alhakin shan kayen Najeriya a Rasha kan rashin dabara

media
'Yan wasan Crotia, yayinda suke murnar kwallon da dan wasan Najeriya Oghenekaro Etebo ya ci gida a bisa kuskure, a wasan farko da suka fafata na gasar cin koin duniya, a filin wasa na Kaliningrad, Russia. Reuters

‘Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akan rashin nasarar da tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles ta yi, a wasan farko da ta buga na gasar cin kofin duniya tsakaninta da Croatia.


Mafi akasarin magoya bayan ‘yan wasan na Super Eagles sun nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin Najeriya a wasan da ta yi rashin nasarar da 0-2.

Tsohon gwarzon dan wasan Super Eagles Jay Jay Okocha, na daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan wasan na ranar Asabar,inda ya dora alhakin kayen da Najeriya ta sha akan rashin dabara a bangaren mai horarwa da kuma ‘yan wasan.

Okocha, wanda ya bayyana haka yayin zantawarsa da gidan talabijin na Super Sports, ya ce ‘yan wasan Najeriya sun buga wasan ne a guraben da basu saba taka leda ba, lamarin da ya sa suka gaza nuna bajintarsu.

Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayar da misalin cewa kama ta yayi, kaftin din tawagar Super Eagles Mikel Obi, ya buga bangaren dan tsakiya mai tsaron gida, kamar yadda ya ke yi a lokacin da yake kungiyar Chelsea, amma ba sashin dan tsakiya mai jefa kwallo ba.

Okocha ya kara da cewa Alex Iwobi, wanda a halin yanzu shi ne mafi kwarewar dan wasan tsakiya a tsakanin ‘yan wasan na Super Eagles, kamata ya yi a wasan na ranar Asabar, ya buga bangaren tsakiyar, amma ba gefe ba.

A ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki Najeriya za ta fafata da Iceland, yayinda kuma a ranar 26 ga watan za ta buga da Argentina.