Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda na zanga-zanga a birnin Maiduguri

Hatsaniya ta kaure a birnin Maiduguri na jihar Borno da ke Najeriya bayan jami’an ‘yan sandan da aka girke don gudanar da ayyuka na musamman sun shiga wata zanga-zanga tare da datse hanyoyi don nuna bacin ransu game da rashin biyan su kude-kuden alawus-alawus har na tsawon watanni shida.

Jami'an 'yan sandan sun datse babbar hanya a birnin Maiduguri don nuna bacin ransu kan rashin biyan su hakkokinsu na watanni shida
Jami'an 'yan sandan sun datse babbar hanya a birnin Maiduguri don nuna bacin ransu kan rashin biyan su hakkokinsu na watanni shida Reuters/A.Sotunde
Talla

Rahotanni na cewa, jami’an sun yi ta harbe-harbe a sararin samaniya a safiyar yau Litinin, lamarin da ya tilasta wa matuka motoci da sauran jama'a tserewa don fakewa a wasu wurare.

Jaridun Najeriya sun rawaito jami’an na cewa, ba za su iya ci gaba da lamuntar rashin biyan su hakkokinsu ba har na tsawon watanni shida.

‘Yan sandan sun ce, ba su da wurin kwana mai kyau, lamarin da ya sa suke barci a filin Allah Ta’ala.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Borno, Damian Chukwu ya shaida wa manema labarai cewa, rashin biyan kudaden na da nasaba da jinkirin da aka samu wajen rattaba hannu kan kasafin 2018.

An girke jami’an ne don agazawa wajen yaki da mayakan Boko Haram da ke tayar da kayar baya a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.