rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Abuja

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan fashi sun kashe jami'an 'yan sanda a Abuja

media
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aikinsu REUTERS/Afolabi Sotunde

Wasu ‘yan fashi da makami sun kashe jami’an ‘yan sandan Najeriya bakwai a babban birnin kasar, Abuja.


Rahotanni na cewa lamarin ya auku ne a yammacin yau Talata a mahadar hanyar Galadimawa da ta ratsa hanyar filin jiragen sama na kasa da kasa.

Kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, Sadiq Bello ya tabbatar wa manema labarai da aukuwar lamarin duk da cewa bai bada cikakken bayani ba.

Tuni aka kwashe gawarwakin 'yan sandan, yayin da mazauna yankin suka shiga halin firgici.

Bayanai na cewa, 'yan fashin da ke cikin mota sun far wa 'yan sandan ne cikin ba-zata a dai dai lokacin da suke bakin aiki.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku da aka kashe wasu jami’an ‘yan sanda a Akwa Ibom da ke kudancin kasar.