Isa ga babban shafi

Tattaunawar shugaba Macron da sashin Hausa na RFI

A ranar Laraba 4 ga watan Yuli na shekara ta 2018, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kawo karshen ziyarar kwanaki biyu da kai a Najeriya, AbdoulKareem Ibrahim Shikal na Sashin Hausa na Radio France International RFI, ya tattauna da shugaban kan wasu manyan batutuwa da suka hada da Tattalin arziki, yaki da ta'addanci, da kuma bunkasa alakar ala'adu tsakanin Faransa da Najeriya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. RFI
Talla

Tambaya

Shugaba Emmanuel Macron, a ranar Talata ka gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda daga bisani ku ka sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama, ko za ka yi mana karin bayani a game da wadannan yarjeniyoyi?

Amsa

Lalle mun sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama da shugaba Buhari a jiya, abu mai muhimmaci a gare mu shi ne tabbatar da tsaro, musamman taimaka wa sojojin da ke yaki da Boko Haram.

To sai dai har kullum fatanmu shi ne fadada wannan alaka domin taimaka wa Najeriya don samun nasara a wasu fannoni, wannan ne ya sa muka kulla yarjeniyoyi da dama, ta farko taimaka wa jihar Legas don inganta sufuri da kuma gine-gine, sai kuma taimaka wa Najeriya don samar wa al’umma ruwan sha musamman a arewacin kasar.

Akwai wani gagarumin shiri na taimaka wa kasar domin kare gandayen daji, da habaka aikin gona, da kuma wasu ayyuka da za mu yi da hadin gwiwar ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

Tambaya

Kana gudanar da wannan ziyara ce a daidai lokacin da rikici ke cigaba da yaduwa a yankunan da ke amfani da turancin Ingilishi na kasar Kamaru, ko meye matsayin Faransa a game da wannan rikici?

Amsa

Yana da kyau musani cewa ba aikin Faransa ba ne shata wa kasashe abin za su yi, to amma na zanta ta wayar tarho da shugaba Paul Biya kafin taron Kungiyar Tarayyar Afirka, fatana shi ne Kamaru ta samar da mafita dangane da rikicin, wannan kuwa ba zai yiyu ba sai tare da bai wa kowane rukuni na jama’a matsayinsa.

Duk inda ka je a Afirka, za ka tarar cewa akwai irin wannan rukuni na tsiraru a cikin al’umma, abin da suke bukata shi ne ba su damar samun ilimi, mutunta al’adunsu da kuma damawa da su a fagen tattalin arziki.

Ya kamata a shimfida kyakkyawar siyasar da za ta bai wa kowa matsayinsa a kasar Kamaru, kuma ina zaton cewa wannan ce manufar Paul Biya.

Tambaya

Kana ziyara a Najeriya, daya daga cikin kasashen da shirye-shiryen Sashen Hausa na rfi ke isa ga milyoyin mutane, me za ka ce a game da wannan rediyo?

Amsa

Da farko ina son ka ba ni dama don isar da sako irin na zumunci zuwa ga illahirin masu sauraren RFI hausa, wannan harshe ne mai matukar muhimmanci, kuma ina sane da irin matsalolin da al’ummar wannan yanki ke fama da su, da suka hada da talauci da kuma mafin munin ayyukan ta’addanci.

Abu ne mai kyau a samu kyakkyawar mu’amala tsakanin harshen Faransanci da sauran harsunan Afirka, musamman ma harshen Hausa, ina jinjina maku sosai lura da irin gagarumin aikin da sashen hausa na rfi ke gudanarwa.

Wannan alama ce da ke kara tabbatar da cewa abu ne mai kyau a samu irin wannan musaya ta al’adu da kuma harsuna. Shugaba Buhari da kansa ya ce lokuta da dama yana sauraren sashen Hausa na rfi.

Tambaya

Jama’a a wannan yanki na fama da matsaloli da dama, ba ka ganin cewa akwai bukatar kara mayar da hankali kan wasu abubuwa na cigaba a maimakon batun tsaro kawai?

Amsa

Za mu cigaba da yaki da masu ikirarin jihadi da kuma ‘yan ta’adda, za mu yi wannan yaki ne ta hanyar amfani da karfin soji, to amma yana da kyau a yi nazari a game da matsalolin da ke sa jama’a na fadawa a ci kin wannan mummunan hali sakamakon rashin abin da za su yi a rayuwarsu ta yau da kullum. Zan ci gaba da taimakawa gwamnatocin Afrika domin tunkarar matsalolin da al’ummominsu ke fama da su.

Bari in sake yin amfani da wannan damar domin isar da sako na zumunci ga wadanda ke jin harshen Hausa sannan kuma suke saurarenku a koda yaushe.

‘Ina yi ma ku godiya’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.