rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari PDP APC

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar nPDP ta kafa sabuwar jam'iyyar APC

media
Alhaji Buba Galadima shugaban sabuwar jam’iyyar APC, da aka sanya wa sunan R-APC. NewsLocker

Tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da ke APC, wato ‘yan kungiyar nPDP, sun kafa sabuwar jam'iyyar APC da suka sanya wa suna (R-APC).


Kungiyar ta nPDP ta bayyana daukar matakin ne yayin ganawa da manema labarai otal din Sheraton da ke Abuja, a ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Yayin sanarwar, tsaffin ‘yan jami’yyar PDP da ke APC sun bayyana Alhaji Buba Galadima a matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar ta R-APC, Dakta Atanda a matsayin sakataren jam’iyyar, sai kuma Kazeem Afegbua a matsayin sakataren yada labaran jam'iyyar.

Yayinda ya ke yi wa manema labarai karin bayani, Alhaji Buba Galadima, ya ce tilas ce ta saka su daukar wannan mataki, la’akari da cewa jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sun gaza sauraron kokensu na mayar da su saniyar ware.

Galadima ya kara da cewa R-APC jam’iyya ce halastaciyya, wadda ba ta bukatar tunkarar hukumar zaben Najeriya domin yi mata rijista, zalika duk wanda bai gamsu da matakinsu na kafa jam’iyyar ta R-APC ba, ya na da damar garzayawa kotu.

A cikin watan Mayu da ya gabata, Shugabannin kungiyar nPDP, wadanda suka fice daga tsohuwar jam’iyyar da ta mulki Najeriya tsawon shekaru 16 kafin zuwan Muhammadu Buhari karagar mulki, suka gindaya sharudda domin cigaba da kasancewa a jam’iyyar APC.

Daga cikin sharuddan da suka gindaya sun hada da janye kararrakin da aka shigar a kan shugaban majalisar dattawan kasar Abubakar Bukola Saraki, da bai wa kakakin majalisar wakilan tarayya Yakubu Dogara da tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso damar samun gurabu a zaben share fage da jam’iyyar APC ta gudanar a jihohinsu.

Sauran sharuddan da gungun na nPDP ya gindaya bayan ganawa da mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, sun hada da kawo karshen abinda suka kira tursasawa da hukumar yaki da rashawa EFCC ke yi wa wasu daga cikinsu, sannan kuma da jan kunne babban sufeton ‘yan sanda kasar sakamakon kin gurfana gaban majalisar dattawa duk da sammacin da aka tura masa.

Tun a waccan lokacin ne kungiyar ta nPDP ta ce matukar aka kai karshen watan Yuni ba tare da warware matsalolin ba, to ko shakka babu matsalar za haifar da rashin hadin kai tsakanin ‘yayan jam’iyyar APC kafin zaben shekara mai zuwa.