rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar addinin Musulunci ta Najeriya ta yi tir da kashe kashen da ke wakana a kasar.

media
Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad, Sultan of Sokoto, Nigeria Daily Trust/Nigeria

Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Najeriya karkashin jagorancin Mai Alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana bacin ranta, dangane da kashe-kashen da ke faruwa a kasar.


Sanarwar da majalisar ta fitar a yammacin jiya alhamis, ta bayyana kashe-kashen mutane na baya bayan nan da aka yi a jihar Plateau na matsayin abin asha, wanda kafin nan aka aikata makamantansu a jihohin Taraba, Benue, Nasarawa da kuma Zamfara.

Majalisar ta yi tir da Allah wadai da tashe-tashen hankulan, inda ta bukaci a gaggauta kawo karshensu.

Sanarwar ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin jihar Plateau, musamman dangen da irin matakan da take dauka domin gurfanar da wadanda ke ruruwa wutar rikici da suna addinin a jihar, tare da yin kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta samar da tsaro musamman a yankunan karkara, sannan da sake fasalta sha’anin tsaro a kasar baki daya.

Har ila yau Majalisar ta Musulunci a Njeriya, ta ce a mafi yawan lokuta musulmi ne suka fi rasa rayukansu, hatta ma a hare-haren da ake dangantawa da makiyaya a sassan kasar.

Sanarwar ta ce ba ta yadda za a samu zaman lafiya da cigaba sai an hada hannu, tare da cigaba yin addu’o’i.