rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnan Ekiti ya zargi 'yan sanda da yunkurin hallaka shi

media
Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose. Pulse.ng/Twitter/@OfficialPDPNig

Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaben Gwamnan Ekiti a Najeriya, Gwamnan jihar Ayodele Fayose, yayi zargin cewa ‘yan sandan da aka tura jihar don zabe na take-taken hallaka shi.


Wasu da suka shida abinda ya faru sun ce, gwamna Ayodele Fayose wanda ke daya daga cikin gwamnonin da ke cikin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya nemi shiga da karfin tsiya inda ake wani gangami ne don marawa dan takararsa baya a zaben na gwamnan wato Kolapo Olusola, amma ‘yan sanda suka hanashi.

Daga bisani ne ‘yan sandan suka fesa hayaki mai sa hawaye don fasa taron gangamin, duk da cewa gwamnan jihar ta Ekiti Fayose yana wajen.

Bayan aukuwar lamarin ne gwamnan daure da bandeji a wuya, da hannu ya bayyana gaban manema labarai yana rusa kuka, inda ya ce yana bukatar duniya ta sani cewa ‘yan sanda na neman hallaka shi.