Isa ga babban shafi
Najeriya

An samu karuwar wadanda suka mutu a hare-haren Sokoto - Tambuwal

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya ce yawan wadanda suka hallaka sakamakon hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a jihar ya karu zuwa 39 daga 32.

An samu karuwar yawan wadanda 'yan bindiga suka hallaka a Sokoto.
An samu karuwar yawan wadanda 'yan bindiga suka hallaka a Sokoto. Information Nigeria
Talla

Tambuwal wanda ke karbar bakuncin wasu gwamnoni a jihar domin jimamin faruwar al’amarin, yace an gano karin wasu gawarwakin ne bayan da aka yi jana’izar mutane 32 da suka hallaka da farko.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci ta’aziyyar akawi Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar, Gwamnan Katsina Aminu Masari, da kuma na Adamawa, Jibrila Bindow.

A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare kan kauyukan Gandi da Mabanni, wadanda ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, inda suka hallaka rayuka da dama, tare da lalata dukiya mai tarin yawa.

Gwamnan jihar ta Sokoto yace a halin da ake ciki, mutane 10, 000 ne da suka rasa muhallansu a kauyukan da aka kai hare-haren, ke gudun hijira a wasu sansanoni da aka kafa musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.