rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki Sufuri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta gabatar da jirgin samanta a London

media
Jirgin saman Najeriya mai suna "Nigeria Air" zai fara a ranar 19 ga watan Disamba mai zuwa stuntfm.com

Gwamnatin Najeriya ta gabatar da sabon jirgin sama na kasar a wani bikin baje kolin jiragen sama da ke gudana a birnin London.


Karamin Ministan jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ne ya wakilci gwamnatin kasar wajen gabatar da jirgin saman mai suna "Nigeria Air.”

A yayin gabatar da jawabi , Sirika ya ce, wannan ranar ce mai matukar muhimmanci ga Najeriya wadda ta kasance mai mafi karfin tattalin arziki da yawan al’umma a Afrika.

Ministan ya koka kan yadda kasar ta shafe tsawon shekaru ba tare da zirga-zirgar jirgin sama na kasar ba.

Sai dai gwamnatin Najeriya ba za ta mallaki fiye da kashi biyar na jirgin ba, lura da cewa za a mika ragamar tafiyar da shi ne a hannun ‘yan kasuwa da suka zuba hannayen jari a cikinsa kamar yadda Sirika ya bayyana.

Ana saran gabatar da jirgin a Najeriya a hukumance a ranar 19 ga watan Disamba mai zuwa, in da zai rika zirga-zirga akan hanyoyi 81 da suka hada da cikin gida da waje.

Tambarin jirgin na dauke da launin kore da fari.