An kama wasu 'yan Boko Haram da suka sace daliban Chibok
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kame wasu muhimman ‘yan kungiyar Boko Haram 22, da suka taka rawa wajen sace daliban makarantar ‘yan matan sakandiren Chibok 276 da ke jihar Borno a shekarar 2014.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno damian Chukwu, ya ce sun samu nasarar kame ‘yan Boko Haram din ne, bayan shirya dabaru sosai, tare da amfani da fasahohin zamani, a tsakanin 4 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan na Yuli cikin wannan shekara ta 2018.
Wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya aiko mana da rahoto akai.
An kama wasu 'yan Boko Haram da suka sace daliban Chibok
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu