Isa ga babban shafi
Najeriya

An kama mutane 117 bisa alakarsu da hare-haren Zamfara

Rundunar ‘yan sandan Zamfara, ta sanar da samun nasarar kama mutane 117, wadanda ta ke zargi da hannu wajen hare-haren ‘yan bindiga ke kaiwa a sassan jihar.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. REUTERS/Austin Ekeinde
Talla

Yayin sanar da kamen, kakakin rundunar, Muhd Shehu, ya ce sun kame wadanda ake zargin ne a wani samame da suka kai kan maboyarsu.

Kakakin ‘yan sandan ya ce 72 daga cikin wadanda aka kama, sun kware, wajen amfani da babura marasa rijista, wajen safarar mutanen da suka sace zuwa maboyarsu.

Kamen dai ya zo kwanaki kadan, bayan da wasu barayin shanu bisa babura suka kai hare-hare kan wasu kauyukan karamar hukumar Maradun da ke jihar ta Zamfara, inda suka yi awon gaba da dabbobi masu yawa, bayan hallaka akalla mutane 30, kamar yadda wasu mazauna kauyukan da abun ya shafa suka bayyana.

Sai dai daga bisa ni rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ta musanta cewa yawan wadanda suka hallaka bai kai hakan ba, inda ta ce mutane uku ne kawai suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.