Isa ga babban shafi
Najeriya

Tilas Saraki ya sauka daga shugabancin majalisar dattijai - Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomhole ya ce tilas Bukola Saraki ya sauka daga mukamin shugaban majalisar dattijan kasar, sakamakon sauyin shekar da ya yi zuwa jam’iyyar PDP a ranar Talata, 31 ga watan Yuli na 2018.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki. REUTERS/Paul Carsten
Talla

Oshoimhole ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a garin Abuja, jim kadan bayan jagorantar wasu sanatoci karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, wajen ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Taron da ya gudana a ranar Larabar na da ta gabata, ya mayar da hankali ne kan sauyin shekar da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC mai mulki da suyka yi zuwa PDP.

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da ficewa daga APC zuwa PDP.

Matakin na Tambuwal, ya sa yawan gwamnonin jam’iyyar APC da suka fice zuwa PDP karuwa zuwa uku.

Kafin daukar matakin na gwamnan Sokoto, gwamnonin jihohin Benue da na Kwara suka fara sauyin shekar, wato Samuel Ortom, da Abdulfatah Ahmed.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.