Isa ga babban shafi
Najeriya

Yawan wadanda ke neman takarar shugaban kasa a PDP ya karu

Gwamnan jihar Gombe Hassan Dankwambo ya bayyana aniyar tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

Gwamnan Jihar Gombe Hassan Dankwambo.
Gwamnan Jihar Gombe Hassan Dankwambo. News Digest
Talla

Gwamnan jihar ta Gombe shi ne mutum na shida da ya bayyana aniyar neman jam’iyyar PDP ta bashi tikitin zama dan takarar ta a zaben shugabancin Najeriya da ke tafe a shekarar 2019.

Sauran ‘yan takarar da suka yi shelar aniyar neman shugabancin Najeriya, sun hada da, tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, Sanata Ahmed Makarfi tsohon gwamnan Kaduna, kuma tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP, da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido.

Sauran ‘yan takarar, sun hada da tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa da kuma Tanimu Turaki tsohon Minista a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Akwai dai wasu karin mutane da ake sa ran cewa nan gaba kadan za su iya bayyana aniyarsu ta neman jam’iyyar adawa ta PDP ta basu tikitin yi mata takara a zaben shugabancin Najeriya na 2019.

Wasu daga cikin jiga-jigan da ake sa ran yin shelar fitowarsu takara sun hada da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Tsohon gwamnan Kano, Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, da kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.