Isa ga babban shafi
Najeriya

An saki tsohon shugaban hukumar DSS daga daurin talala

Jami’an tsaron Najeriya sun saki korarren shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya na DSS Lawal Daura daga tsare shin da aka yi a daya daga cikin gidajen saukar baki dake fadar shugaban kasa.

Korarren shugaban hukumar jami'an tsaron farin kaya na DSS Lawal Daura.
Korarren shugaban hukumar jami'an tsaron farin kaya na DSS Lawal Daura. The Guardian Nigeria
Talla

Rahotanni daga Najeriyar sun ce kafin sakin tsohon shugaban jami’an farin kayan, sai da aka kwace fasfo dinshi na tafiye-tafiye domin haramta mishi ficewa daga kasar.

Wasu rahotannin da ke fitowa daga Najeriyar sun ce mai yiwuwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta binciki tsohon shugaban na DSS, sakamakon wasu zarge-zarge da ake masa na aikata laifukan na cin hanci da rashawa.

A baya dai fadar shugabancin Najeriya ta ce korarren shugaban hukumar jami’an tsaron farin kaya na DSS, lawal Daura zai cigaba da zama a tsare a karkashin daurin talalar da aka yi masa.

Wata majiya daga fadar shugaban Najeriya ta ce ana tsare da Lawal Daura tun a lokacin da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kore shi daga mukaminsa, inda nan take jami’an ‘yan sandan kasar suka tsare shi a daya daga cikin gidajen saukar baki fadar shugaban kasar.

Majiyar da ta nemi a sakaya ta, ta ce shugaban hukumar ta DSS, zai ciga da ma a tsare, har sai an kammala gudanar da jerin bincike akan zarge zargen da ake masa bisa al’amura daban daban.

Bayanai sun tabbatar da cewa, bayaga laifin datse kofar shiga zauren majalisun tarayyar Najeriya, gwamnatin tarayya za ta binciki Lawal Daura kan wasu matakai da ya dauka a baya, da suka shafa mata bakin fenti, ciki harda matakin da ya dauka na baiwa jami’an DSS umarnin kai samame gidajen wasu manyan alkalai a watan Oktoban shekara ta 2017, bayan da aka zarge su da laifin cin hanci da rashawa.

A ranar Talata, 7 ga watan Agusta, 2018, Lawal Daura ya gana da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, jim kadan bayan kawo karshen datse shiga zauren majalisar dokokin kasar da ya bada umarnin yi, mukaddashin shugaban ya kore shi daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.