Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a tsige Saraki ta hanyar bin doka - Oshiomhole

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta baiwa shugaban majalisar dattijan kasa Bukola Saraki gajeren wa’adi na ya yi murabus daga mukaminsa ko kuma a tsige shi.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban jam’iyyar ta APC Comrade Adams Oshiomhole, yayi gargadin cewa basu da wani zabi da ya wuce fara shirin tsige Sarakin, muddin ya ci gaba da dagewa kan jagorantar majalisar dattijan, duk da komawarsa jam’iyyar PDP.

Yayin sanar da matakin, Comrade Oshiomhole ya ce za’a tsige Bukola Saraki ne, ta hanyar doka, sabanin zargin da ake musu na shirin bi ta kowane hali wajen cimma burinsu.

Jim kadan bayan ganawar Oshiomhole da ‘yan jaridu ne shugaban majalisar dattijan Bukola Saraki, ya ce ikirarin shugaban jam’iyyar ta APC da sauran mutanen da ke burin saukarsa daga jagorancin majalisar, mafarki kawai suke yi, wand aba zai zama gaskiya ba.

A nata bangaren yayin da take mayar da martani jam’iyyar adawa ta PDP, ta ce APC ba ta da yawan ‘yan majalisun da ta ke bukata wajen tsige Saraki, da mataimakinsa Ike Ekweremadu dan haka ta hakura ta gaskiyar abinda ke kasa, a cewar kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan.

APC na bukatar samun goyon bayan akalla sanatoci 73 a zauren majalisar dattijan kafin samun nasarar tsige Saraki daga kujerarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.