Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yiwa 'yan sanda kwanton-bauna a Kaduna

Wasu masu satar mutane suna garkuwa da su domin karbar kudi a Jihar Kaduna dake Najeriya, sun kashe jami’an ‘yan sanda guda 4, a lokacin da suka yi musu kwanton bauna a dajin Rigasa.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. Reuters
Talla

Bayanai sun ce, ‘yan Sandan sun kama biyu daga cikin gungun masu garkuwa da mutanen, wadanda ake zargin sun sace fitatccen malamin Kaduna Sheikh Ahmad Adam Algarkawy, wanda suka sako daga baya.

A makon da ya gabata, ranar 2 ga watan Agusta ‘yan bindigar suka sace malamin a unguwar Rigasa, daga bisani kuma suka sako shi a ranar 6 ga watan na Agusta, bayan da rahotanni suka ce iyalansa sun biya akalla naira miliyan 10 a matsayin fansa.

Shugaban tawagar rundunar dake yaki da aikata manyan laifufuka ta musamman, Abba Kyari ya tabbatar da harin kwanton baunar da aka yiwa jami’an nasa, inda ya ce jami’i guda ya samu rauni, yayinda su kuma suka samu nasarar hallaka 6 daga cikin ‘yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.