Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta kora mutanen Najeriya zuwa Kamaru

Rohotanni daga Najeriya na cewa, daruruwan jama’a na tserewa daga gidajensu da ke garin Gamboru Ngala na jihar Borno, in da suke neman mafaka a kasar Kamaru sakamakon yadda mayakan Boko Haram suka shafe fiye da kwanaki 10 suna karkashe jama’a a garin.

Wasu daga cikin mutanen da Boko Haram ta tilasta wa tserewa daga gidajensu
Wasu daga cikin mutanen da Boko Haram ta tilasta wa tserewa daga gidajensu REUTERS/stringer
Talla

Wani mazaunin garin Mohammadu Miloniya ya shaida wa sashen Hausa na RFI cewa, mayakan sun kwashe kwanaki 12 suna yi wa mutane kisan gilla tare da sace dukiyoyinsu.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren muryar da ke bada shedar ta'asar Boko Haram a garin Gamboru Ngala.

02:56

Saurari muryar da ke shaida yadda Boko Haram ke ta'asa a Gamboru Ngala

Miloniya ya bayyana fargabar cewa, mayakan ka iya mamaye garin baki daya don kafa tungarsu, lura da yadda suke cin karansu babu babbaka.

Miloniya ya zargi jami’an tsaro da gazawa wajen kawo musu dauki duk da cewa, suna kusa da in da Boko Haram ke tafka ta'asar.

Ba a karon farko kenan ba da kungiyar Boko Haram ke kai hare-hare a kauyuka daban daban da ke jihar Bornon Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.