Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya kammala hutunsa a London

Wani lokaci a yau Asabar ake sa ran shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai koma gida daga gejeren hutun da ya dauka zuwa birnin London.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS /Stringer
Talla

Sai dai yayin bada tabbacin komawar shugaban Najeriyar Gida, kakakinsa Malam Garba Shehu bai bayyana ainahin lokacin da shugaba Buhari zai isa kasar ba.

Tun a ranar 3 ga watan Agusta, 2018, shugaban ya fara hutun kwanaki 10 a birnin London inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar a matsayi mukaddashin shugaba.

Daga cikin muhimman ayyukan da mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo ya zartar akwai sauya shugabancin hukumar jami’an tsaron farin kaya ta DSS, inda ya maye gurbin Lawal Daura da Mista Matthew Seiyefa.

Korar Lawal Daura daga mukaminsa ya biyo bayan umarnin da ya baiwa jami’an hukumar ta DSS na datse kofar shiga majalisun Najeriya a farkon watan Agusta , lamarin da haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar.

Farfesa Osinbajo, ya kuma bada umarnin sauya fasalin shugabanci da ayyukan rundunar ‘yan sandan kasar ta musamman mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka wato SARS.

Umarnin yiwa rundunar garambawul ya biyu bayan koken jama’a da ya yawaita, kan yadda jami’an ‘yan sandan da ke karkashin rundunar ta SARS ke cin zarafin mutane yayin gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.