rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsaikon kasafin kudi ba zai sanya a canza ranakun zabe ba - INEC

media
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu daga tsakiya. Ventures Africa

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ba za a sauya jadawali, ko ranar da za’a soma zabukan kasar masu zuwa a shekarar 2019 mai kamawa ba.


Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne, yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya jaddada cewa tsaikon da hukumar ta INEC ke fuskanta daga majalisun tarayyar Najeriya wajen amincewa da kasafinta na Naira biliyan 189 ba zai sanya ta matsar da ranar 16 ga watan Fabarairu na 2019 da ta tsara zaben zai soma ba.

A jiya juma’a ne dai hukumar zaben Najeriyar ta fitar da jadawalin yadda al’amuran zaben kasar da ya shafi jam’iyyun siyasa da ‘yan takara za su gudana kafin gudanar da zaben na 2019.

Daga ciki akwai mikawa ko karbar takardun takara a zabukan matakin kasa ko jiha da jam’iyyu za su yi, wanda hukumar ta INEC ta tsayar da wa’adin 17 ga watan Agusta da muke ciki zuwa 24 ga watan.

Shugabar sashin wayar da kan jama’a dangane da ayyukan hukumar ta INEC Ndidi Okafor ta kara da cewa, hukumar ta tsayar da ranar 17 ga watan Nuwamba mai zuwa a matsayin wa’adin karshe na janye sunan dan takara ko sauya shi a matakin neman shugabancin kasa ko takarar shiga zauren majalisun tarayya.

Zalika ranar 1 ga watan Disamba, ita ce wa’adin karshe na sauya ‘yan takara ko janye su a matakin neman kujerar gwamna ko takarar kujerun zauren majalisun dokokin jihohi.