Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya baiwa soji umarnin kada su tausayawa 'yan bindiga

Shugaban Najeriya Muhd Buhari ya baiwa rundunar sojin kasar ta musamman dake yakar barayin shanu a jihar Zamfara, umarnin kada su nuna tausayi yayin kokarin murkushe ‘yan bindiga a jihar da sauran sassan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. RFIHausa/Kabiru Yusuf
Talla

Shugaba Buhari ya bada umarnin ne a yau Asabar a filin jiragen sama na jihar Katsina, yayin da yake gabatar da jawabi ga rundunar jami’an sojin kasar ta musamman da ta kunshi dakaru 1000 da aka samar domin murkushe hare-haren ‘yan bindiga da sauran manyan laifuka musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya da ya hada da jihar Zamfara.

A yau Asabar 25 ga Agusta, 2018, shugaba Buhari ya koma fadar gwamnati da ke Abuja, domin ci gaba da aiki, bayan kare hutun Sallah Babba a gida.

Tun a ranar 29 ga watan Yuli da ya gabata, Gwamnatin Najeriya ta kafa wata runduna ta musamman da ta kunshi sojin kasa da na sama, da kuma ‘yan sanda da jami’an tsaron hukumar Civil defence domin kawo karshen hare-haren ‘yan bindigar.

Rahotanni daga Najeriyar a yau Asabar sun ce jiragen yakin kasar da ke aiki da rundunar ‘Operation Dirar Mikiya’ mai yaki da ‘yan bindiga a Zamfara sun yi nasarar lalata wasu sansanonin barayin shanu da masu garkuwa da mutane, a kauyukan Bawar Daji da kuma Sunke da ke jihar.

Cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar, ya ce an samu nasarar kai samamen ne bayan samun rahotanni sirri, kan maboyar ‘yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.