Isa ga babban shafi
Najeriya

Sifeton 'yan sandan Najeriya ya takaita ayyukan rundunar FSARS

Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bada umarnin takaita ayyukan jami’an rundunar FSARS zuwa yaki da laifukan fashi da makami da kuma sata da garkuwa da mutane.

Shirin yiwa rundunar 'yan sandan Najeriya ta SARS garambawul ya soma kankama.
Shirin yiwa rundunar 'yan sandan Najeriya ta SARS garambawul ya soma kankama. CGTN Africa
Talla

Umarnin na kunshe ne cikin sanawar da kakakin rundunar ‘yan sandan ta Najeriya Jimoh Moshood ya fitar, wadda cikinta aka umarci jami’an na FSARS da su koma sanya cikakken kakin ‘yan sanda, har zuwa lokacin da za a fitar musu da nasu.

Umarnin wanda ya soma aiki a nan take ya ce daga Yanzu jami’an rundunar na FSARS ba zasu sake tsoma kansu cikin batutuwan da suka shafi zamantakewar fararen hula ba, ciki harda batun kasuwanci.

Kimanin makwanni biyu da suka gabata ne dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta sauya sunan rundunar ta SARS zuwa FSARS a ci gaba da matakan yi mata sauye-sauye.

Matakin dai ya biyo bayan umarnin da matakimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar na yiwa rundunar FSARS mai yaki da manyan laifuka a kasar garambawul, sakamakon yawaitar koke daga la’umma dangane da yadda hami’an rundunar ke amfani da karfin da aka basu wajen cin zarafin al’umma.

A baya bayan nan ne dai sabon kwamishinan rundunar ta FSARS na tarayyar Najeriyar, Habiru Gwandu ya ce tuni aka kafa sashin sauraron kararrakin tauye hakkin dan adam a dukkanin hedikwatocin hukuma ko rundunar ta FSARS da ke sassan kasar, bayaga sauya sunan rundunar.

Gwandu ya kara da cewa, rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara aiki tare da kwararrun likitocin kwakwalwa da kuma masana halayyar dan adam, wajen tantance wadanda yakamata a dauka a matsayin jami'an na rundunar ta musamman ta FSARS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.