Isa ga babban shafi
Najeriya

Ina da kwarin gwiwar zama dan takarar PDP a 2019 - Makarfi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP sanata Ahmed Makarfi, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa shi ne zai yi nasarar samun amincewar jam’iyyar wajen zama dan takararta a zaben shugabancin Najeriya na 2019.

Tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Ahmed Makarfi, yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Ahmed Makarfi, yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Premium Times
Talla

Makarfi ya bayyana kwarin gwiwar tasa ce, yayin wata zantawa da ya yi da amnema labarai a birnin Legas, yau Lahadi.

A cewar sanata Makarfi, mallakar dukiya ko kudi ba zai yi tasiri wajen tantance wanda zai tsayawa jami’yyar PDP takara ba a zaben 2019, kamar yadda ‘yan Najeriya da dama ke zato.

Makarfi ya kara da cewa akwai jerin 'yan takarar neman shugabancin Najeriya kuma tsaffin shugabannni, da suka yi nasarar cimma aniyarsu ba tare da tasirin kudi ba, wadanda suka hada da shugaba da ke kan mulki Muhammadu Buhari, tsohon shugaban Olusegun Obasanjo da kuma tsohon shugaba kuma marigayi, Umar Musa 'Yar Aduwa.

Daga cikin dalilan da Makarfi ya zayyana da yake ganin za su bashi dama akan sauran abokan takararsa akwai gogewar da ya ce ya samu ainun a fannin tattalin arziki, sakamakon shafe shekaru 8 yana cikin kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da sha'anin hada-hadar kudade.

Zalika tsohon sanatan ya ce yana da tsananin kishi wajen maido da martabar jam'iyyar PDP, la'akari da rashin rabuwa da ita, a hali na jin dadi ko na wuya.

Zuwa yanzu dai jimillar wadanda suka bayyana aniyar neman takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, ya kai akalla mutane 12, daga ciki kuma akwai, tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.