Isa ga babban shafi
Najeriya

NEMA zata kai dauki zuwa Jihohin Najeriya dake fuskantar iftila'in ambaliyar ruwa

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta shelanta cewa jihohin Kogi, Niger, Delta da kuma Anambra na fuskantar Iftila’in ambaliyar ruwa fiye da sauran takwarorinsu a kasar. Hukumar Agajin gaggawa a Najeriya tace tana daukar matakan da suka dace domin kai dauki ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihohin kasar guda 10.

Wani bangaren hanyar da ta tashi daga garin Lokoja zuwa Abuja, da ambaliyar ruwa ta taba mamayewa a shekarun baya.
Wani bangaren hanyar da ta tashi daga garin Lokoja zuwa Abuja, da ambaliyar ruwa ta taba mamayewa a shekarun baya. Sahara Reporters
Talla

Babban darakatan hukumar ta NEMA Mustapha Maihaja ne ya sanar da daukar matakin, wadda ya ce umarni ne daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Daraktan ya kuma ce tuni hukumar ta NEMA ta sa idanu akan wasu jihohin guda takwas da suma ke fuskantar ambaliyar ruwan a sassansu, domin bibiyar halin da ake ciki.

Yayin da yake yiwa Bashir Ibrahim Idris na RFI Hausa karin bayani kan halin da ake ciki ta wayar tarho, Maihaja, ya ce daukar matakin ya biyo bayan ziyarar gani da ido da suka kai zuwa wasu sassan da iftila’in ya ya aukawa

Sai dai a cewar babban jami’in na NEMA, daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne rashin samun hadin kan wasu daga cikin wadanda ake kokarin ceto su daga hallaka.

01:11

Babban darakatan hukumar NEMA ta Najeriya Mustapha Maihaja

Bashir Ibrahim Idris

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.