Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu siyasa a matakin haramta amfani da wayoyi a rumfunan zabe - INEC

Hukumar shirya zabukan Najeriya mai zaman kanta INEC, ta yi karin bayani akan matakin da ta dauka na haramta amfani da wayoyin hannu hadi da na’urorin daukar hoto a rumfunan zabe.

Hukumar shirya zabukan Najeriya ta sha alwashin kawo karshen matsalar saye da sayarwar kuri'u yayin gudanar da zabuka a matakai daban daban.
Hukumar shirya zabukan Najeriya ta sha alwashin kawo karshen matsalar saye da sayarwar kuri'u yayin gudanar da zabuka a matakai daban daban. nigeriannewsdirect.com
Talla

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da duk wani yunkuri na wani ko wata kungiya, wajen shafa mata bakin fentin cewa ta dauki matakin ne, domin cimma wata manufar siyasa.

A lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Abuja, babban sakataren yada labaran hukumar ta INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce, INEC ba ta hana kowa zuwa da wayoyi harabar rumfunan zabe ba.

A cewar Oyekanmi, haramcin zai soma ne, daga lokacin da mutane suka soma karbar kuri’a domin jefawa a kwatunan zabe, amma da zarar mai kada kuri’a ya matsa daga cikin rumfar zaben, yana da damar cigaba da amfani da waya ko kuma na’urarsa ta daukar hoto.

Babban sakataren hukumar ta INEC, yayi wannan karin hasken ne, a lokacin da yake maida martani kan kalaman shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus, wanda yayi amfani da kakkausan harshe wajen sukar matakin na INEC, wanda ta kare kanta da cewa ta dauka ne domin kawo karshen matsalar saye da sayarwar kuri’u, yayin gudanar da zabuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.