Isa ga babban shafi
Najeriya

ASUU ta nemi Naira Triliyan 1 daga gwamnatin Najeriya

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU, ta bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta cika alkawarin da ta dauka na biyanta naira triliyan 1 da doriya, da aka tsara za’a yi amfani da su wajen gudanar da jami’o’in tarayyar Najeriyar.

Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki muddin gwamnatin Najeriya ta gaza cika mata alkawarin da ta dauka.
Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki muddin gwamnatin Najeriya ta gaza cika mata alkawarin da ta dauka. The Herald Nigeria
Talla

Yayin da yake yiwa manema labarai karin bayani a garin Jos da ke jihar Filato, shugaban sashin gudanarwar kungiyar ta ASUU na yankin Bauchi, Farfesa Lawan Abubakar ya ce tuni suka soma tuntubar sassan kungiyar domin yiwuwar daukar matakin shiga yajin aiki a nan gaba.

Kamar yadda wasu jaridun Najeriya suka rawaito, Farfesa Abubakar ya kuma ce basa bukatar ikirarin da Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed ta yi, na cewa gwamnatin kasar ta amince da baiwa bangaren jami’o’in tarayyar Najeriyar Naira biliyan 20, domin ba wannan suke bukata ba.

Farfesan ya kara da cewa babu shakka Naira biliyan 20 babu shakka ba zasu iya biyan bukatun manyan jami’o’in gwamnatin Najeriya 64 da ake da su a kasar ba, dan haka bukatarsu kawai ita ce naira triliyan daya da ya kamata a baiwa jami’o’in.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.