rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya APC PDP

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zan mara wa Atiku baya a zaben 2019- Obasanjo

media
Tsohon shugaban Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa Abubakar da wasu shugabannin addinai a Najeiya, Mathew Kukah da Sheik Ahmad Gumi RFI/Hausa

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce, ya sauya matsayinsa na rashin goyon bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019.


Mr. Obasanjo ya bayyana haka ne bayan ziyarar da Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka kai masa a gidansa da ke birnin Abeokuta.

Obasanjo ya ce, ya yi amanna cewa, Atiku ya daidaita kansa kuma a yanzu haka ya cancanci samun goyon bayansa a zaben kasar mai zuwa.

Tsohon shugaban na Najeriya ya taya murna ga Atiku game da nasarar da ya samu ta wakiltar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, in da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

A can baya dai, Obasanjo ya lashi takobin rashin mara wa Atiku baya wajen fafutukarsa ta ganin mafarkinsa na zama shugabban kasa ya zama gaske.