Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta sake kashe ma'aikaciyar Red Cross

Kungiyar Boko Haram ta sake kashe daya daga cikin ma’akatan agaji na kungiyar Red cross a Najeriya, Hauwa Liman, yayin da ta lashi takobin ci gaba da bautar da Leah Sharibu, dalibar makarantar Dapchi daya tilo da ke ci gaba da kasancewa a hannun Kungiyar.

Hauwa Liman, ma'aikaciyar Red Cross da Boko Haram ta kashe a Najeriya
Hauwa Liman, ma'aikaciyar Red Cross da Boko Haram ta kashe a Najeriya premiumtimes
Talla

Ministan Watsa labarai na Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da labarin kisan Hauwa Liman, yayin da ya bada tabbaci game da kokarin kubutar da daukacin matan da ke hannun kungiyar.

Mata uku ne ke hannun Boko Haram tun lokacin da aka sace su a garin Rann, hedikwatan Karamar Hukumar Kale Balge, a wani samame da kungiyar ta kai tare da kashe ma'aikatan lafiya uku da da sojoji 8.

Biyu daga cikin matan wato Hauwa Liman da Saifura Khorsa ma'aikatan Kungiyar Agaji ta Red Cross ne, yayin da ta ukun mai suna Alice Loksha ke aiki da Hukumar UNICEF.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.