Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sake jaddada alwashin gudanar da sahihin zabe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayinsa na gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa, wanda kasashen duniya zasu amince da shi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Darren Ornitz/File Photo
Talla

Shugaban ya sake nanata alwashin nasa ne a Abuja, lokacin da yake karbar takardun sabbin jakadun wasu kasashe da aka tura kasar.

Buhari yace Najeriya ta kama hanyar gudanar da zabe bayan guda 5 da akayi a baya daga shekarar 1999 zuwa yanzu, kuma yana da yakinin cewar zaben shekara mai zuwa zai gudana cikin kwanciyar hankali.

Kasashen da suka tura sabbin jakadunsu zuwa Najeriya, sun hada da Japan, Brazil, Rasha, da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.