Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya na gaf da samun tikitin halartar gasar cin kofin Afrika

Najeriya ta samu nasarar karbe ragamar jagorancin rukuni na biyar da take ciki, a wasannin neman cancantar halartar gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika.

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo.
Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo. SuperSport/Gallo Images
Talla

Najeriya ta samu nasarar ce, bayan wasan da ta doke Libya da kwallaye 3-2.

Odion Ighalo da Ahmed Musa ne suka ci wa Najeriya kwallayen, wadanda Ighalo ya ci biyu daga ciki.

A wasan neman cancantar zagayen farko tsakanin kasashen biyu da aka buga a garin Uyo, Najeriya ta lallasa Libya ne da kwallye 4-0.

A halin yanzu Najeriya ke kan gaba a rukuni da take ciki na 5 da maki 9, sai kuma Afrika ta Kudu da maki 8.

Libya ke a matsayi na uku da maki 4, yayinda kasar Seychelles ke matsayin ta karshe da maki 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.